Kotu ta yarda INEC ta sake saita na'urar BVAS don zaɓen gwamnoni
Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta amince da buƙatar hukumar zaɓe ta ƙasar ta sake saita na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaɓen shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabirairu.
BBC ta rawaito cewa tawagar alƙalan kotun mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin Joseph Ikyegh ta yanke hukuncin cewa an bai wa INEC damar ne domin gudanar da zaɓen gwamnoni ranar Asabar 11 ga watan Maris.
Hukuncin na nufin kotun ta ƙi amincewa da buƙatar da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP Peter Obi ya shigar ta neman hana INEC goge bayanan masu zaɓen da aka naɗa a zaɓen shugaban ƙasar.
Tawagar alƙalan ta ce INEC ta bayyana cewa tana da shirin kwashe bayannan da ke cikin na'urar 176,000 da aka yi amfani da su a zaɓen ta wallafa su a wani rumbun bayananta na daban, ko da yake Obi da LP ba su nuna ƙin amincewa da wannan shiri ba.
Tun da fari Mista Obi na jam’iyyar Labour ya shigar da ƙarar INEC a kotu kan zargin hukumar ba ta yi amfani da na’urar BVAS yadda ya dace ba, abin da ya sa suka gaza yin nasara a zaɓen, wanda aka bayyana Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya yi nasara.
Lauyan Obi, Onyechi Ikpeazu, yace dalilin shigar da ƙarar da suka yi shi ne don su cire bayanan da aka wallafa a cikin BVAS ɗin, na ainihin sakamakon da aka wallafa tun daga rumfunan zaɓen.