Kotun, hukuncin bai-ɗaya da mai shari’a Adamu Jauro ya gabatar, kwamitin alkalai 5 ya yi watsi da korafin da aka shigar na kawo wani dan takarar gwamna, Dakta Ibrahim Gusau.
Kwamitin amince da maganar Damian Dodo, mai matsayin SAN, lauya ga Lawal Dare cewa an gabatar da wanda yake karewa bisa doka da ka’ida kamar yadda doka ta tanada.
Jauro ya kuma amince da hukuncin kotun daukaka kara da ta amince da zaben fidda gwani na biyu da ya fitar da dan takarar.
A zaben fidda gwanin dai Lawal-Dare ya samu kuri’u 442, inda ya samu nasara a kan Gusau da sauran yan takara.
Jauro ya ce wata babbar kotun tarayya da ke Gusau wadda ta soke zaben fidda gwani har sau biyu ba ta da hurumi a lokacin da ta yanke hukunci kan karar da Gusau ya shigar.