Kwanan na dai ana jin duk wata sanarwa ta sirri ko zama na musamman da jiga-jigan jam'iyyar APC ke yi wanda hakan ke basu mamaki matuƙa gaya kasancewar waɗanda ake ire-iren wannan zaman dasu ba ƙananu bane manya ne kuma yardaddun jam'iyyar amma kuma sai ya zamana cewa duk ƙaƙantar taron da suka haɗa suka tattauna sai an sami wani ko wasun su sun fitar da sirrin su. Izuwa yanzu dai suna zargin Murtala Sule Garo da fitar da sirrin nasu musamman yaran Ɗanbilki Kwamanda wanda hakan ya jawo cece kuce a tsakanin su. Yanzu dai Ɗanbilki Kwamanda ya fitk da kansa kuma yayi umarni da a dena haɗa hoton GAWUNA da MURTALA GARO kuma yace basa buƙatar taimakon su ko kaɗan.
Ku dena haɗa hoton Gawuna da Sule Garo, Munafiki ne ~ Ɗanbilki Kwamanda
March 13, 2023
0
Ɗanbilki Kwamanda ya fitar da sanarqar cewa a dena haɗa hoton Gawauna da Murtala Garo saboda suna zargin yana munafurtar su.
Tags