Kar a kira ni da 'His Excellency' sai bayan na bar mulki, in ji Zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamnan Katsina
ZaÉ“aÉ“É“en Gwamnan Jihar Katsina, Dikko RaÉ—É—a, ya bayyana dalilin da ya sa ya ce ba ya so a riÆ™a kiran sa “His Excellency” idan aka rantsar da shi ya kama mulkin Katsina a ranar 29 Ga Mayu.
Ya ce zai fi so a riÆ™a kiran sa da “Mr Governor ko kuma Malam Dikko RaÉ—É—a” amma ba ya so a riÆ™a kiran sa da “His Excellency”, har sai bayan ya kammala wa’adin sa tukunna.
Premium Times Hausa ta rawaito cewa RaÉ—É—a ya bayyana haka a ranar Asabar a Abuja, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
An zaÉ“i RaÉ—É—a a Æ™arÆ™ashin APC, ya samu Æ™uri’u 859,892, ya doke Yakubu Lado na PDP, wanda ya samu Æ™uri’u 486,620.
“Ni dai ba na so idan an rantsar da ni a riÆ™a kira na “His Excellency”, saboda kalma ce mai nuna gwamna ya cika komai, ya yi dukkan abin da ya wajaba da wanda ya kamata ya yi, da kuma nauyin da ya wajaba ya sauke.
“Amma idan za a iya kira na da His Excellency É—in bayan na kammala wa’adi na, idan har jama’a sun ga na yi masu ayyuka masu kyau. Don haka ma har gara a riÆ™a kira na Mr Gobernor ya fi min sauÆ™i.
“Ni ina so na ji ni ina daidai da kowa, saboda ba na son ana Æ™aÆ™aba min ‘Excellency’ É—in nan har ana kumbura min kai. Ni zan ma fi so kawai a riÆ™a kira na Malam Dikko RaÉ—É—a.”
Idan an tuna, a 2019 ma Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya cire “His Excellency” a sunan sa. Haka shi ma tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, wanda ya yi mulki daga 2010 zuwa 2018, an riÆ™a kiran sa da “Ogbeni”, maimakon “His Excellency”.
Shi kuwa Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, ana masa laÆ™abi da “Arakunrin”, wato Mister kenan da kalmar Yarabanci.
Da ya ke magana kan ajandar gwamnatin sa, RaÉ—É—a ya ce idan aka rantsar da shi, zai fi maida hankali ne kan matsalar tsaro wadda ta addabi Jihar Katsina.