Kimanin tubabbun ƴan ta'adda 594 ne suka roki ‘yan Najeriya da a yafe musu ayyukan kashe-kashe da su ka yi, wanda ya taka rawa wajen tada zaune tsaye a kasar.
Tsofaffin ƴan ta’addan sun yi wannan roko ne a yayin bikin yaye su, bayan da su ka shafe watanni shida ana yi musu horo a karamar hukumar Kwami da ke jihar Gombe.
An kirkiro da shirin ne mai suna DDR, don farfado da tubabbun ƴan tada kayar bayan da Sojojin Najeriya ke gudanarwa, karkashin 'Operation Safe Corridor'.
Muhammad Abba, daya daga cikin wadanda a ka yaye ɗin, ya yi magana a madadin sauran tubabbun, inda ya ce shirin ya kara musu ilimi kan juriya da addini da wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
"Muna neman afuwar 'yan Najeriya da gwamnatocin jihohin mu daban-daban, al'ummominmu, kuma duk wanda ke zaune a nan ya mika wannan sako namu ga kowa da kowa a al'ummomin da muka fito," NAN ta ruwaito Abba yana cewa.
“Mun yi nadama kuma ba za mu sake koma wa kan wannan ta’asa ba. Mun yi mubaya'a ga kasarmu ta Najeriya mai zaman lafiya," in ji shi.
A cewar kwamandan sansanin, Uche Nnabuihe, uku daga cikin tsaffin ‘yan ta’addan sun fito ne daga jamhuriyar Nijar, inda daya kuma daga kasar Chadi.
Nnabuihe ya ce shida daga cikin ‘yan ta’addan ‘yan tada kayar baya ne kiristoci.
Kwamandan sansanin ya ce 15 daga cikin tsaffin maharan sun fito ne daga Adamawa, Borno, 495; Kano, 16; Yobe, 16; Kaduna, 13; Gombe, 3 da daya daga Kogi.
Mnabuihe ya kara da cewa 12 daga cikin tsaffin ‘yan ta’addan sun fito ne daga Bauchi, biyar kowanne daga Jigawa da Katsina, hudu daga Kebbi, daya daga Nasarawa da Filato, biyu kuma daga Zamfara.