Kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kai ƙorafi ga hukumar yada labarai ta kasa, NBC, inda ya bukace ta da ta sanya wa Channels TV takunkumi.
A cikin koradin da ya shigar, mai dauke da kwanan watan 28 ga watan Maris da kuma mika wa babban daraktan hukumar NBC, kwamitin ya zargi mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, da yin kalamai da dama na tunzuri, wanda ke nuna rashin amincewar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023
Takardar koken mai dauke da sa hannun Bayo Onanuga, ta bukaci hukumar da ta kakaba wa gidan talabijin din takunkumin da ya dace.
A wani bangare na koken na cewa, “A daidai da sashe na 14.0.1 na kundin tsarin yada labarai na Najeriya bugu na 6 da ke bayyana hakkin hukumar yada labarai ta kasa na karbar korafe-korafe da ga al'umma, da yin bincike tare da sanya takunkumi idan ya cancanta. , Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban ƙasa na APC ya shigar da korafi a gaban Hukumar kan abubuwan da ta yi la’akari da karya da CHANNELS TV ta yi a makon jiya a shirinta na ‘Siyasa A Yau’ da ke fitowa kullum da karfe 7 na dare a ranakun mako.
“Shi [Datti] ya ce jam’iyyar Labour ce ta lashe zaben. Wannan karya ce ba daidai ba. Bisa ga ka'ida, mai watsa shirye-shiryen na da laifi idan har ya bar baƙonsa ya yi magana mai ban tsoro da ba daidai ba kuma ba bisa kan gaskiya ba.
"Alkaluman da aka tattara na sakamakon zaɓe na gaskiya shine wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar, wacce ta sanya jam'iyyar Labour a matsayi na uku.
“Bakon shirin da ake magana a kai, Datti Baba Ahmed, ya ce bai kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da zababben shugaban kasa ba saboda bai samu kuri’u kashi 25 cikin 100 na babban birnin tarayya Abuja ba, kasancewar daya daga cikin sharuddan da ake bukata na ayyana shi a matsayin mai nasara.
"Wannan magana ce ta zagon kasa tunda maganar tana gaban kotun kuma tana daga cikin batutuwan da suka mikawa kotuna domin yanke hukunci. Don haka, har sai idan kotu ta yanke hukunci, matsayin da hukumar zabe ta INEC ta bayyana a sakamakon karshe," in ji shi.