Dan Gwamna Nasir El- Rufai, Bashir, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso, ne zai zama “shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaba”.
Kwankwaso ya zo na hudu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda Ahmad Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya lashe.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya zo na biyu yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya zo na uku.
Kwankwaso ya lashe zaben a Kano kadai, inda ya samu kuri’u 997,279, wanda hakan ya sa wasu masu sukarsa ke kiransa da ‘Shugaban Kano’.wasu nace masa Malan Aminun Kano.
A martanin daya bayar a shafinsa na Twitter, dan gwamnan Kaduna ya bayyana cewa: "Masu yiwa Kwankwaso dariya cewa shi shugaban jihar Kano ne kawai ba za su yi dariya ba nan da 'yan shekaru. Shi ne Buhari na gaba, mai yiwuwa."
Dan gwamnan Kaduna ya shahara da bayyana ra'ayinsa a shafukan sada zumunta.
An zabi kanensa Bello a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa.
Bello, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar APC ya doke Samaila Suleiman na jam’iyyar PDP wanda a halin yanzu yake wakiltar mazabar a majalisar wakilai ta kasa.Samaila dai ya koma PDP ne a lokacin da Bello ya rasa tikitin sake tsayawa takara.