Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya musanta labarin cewa ya ƙwace lasisin filin shakatawa na Kano Club dake ƙwaryar birnin Kano, inda yace kawai batu na wata gidan jarida.
Jawabin hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Kano, kwamared Muhammad Garba, inda yace wa'adin doka na bada filin ya ƙare tun a shekarar 2019, amma dukda haka ba'a kwace ba, illa iyaka ma'aikatar ƙasa ta sanar da mamallakan filin ƙarewar wa'adin su.
To sai dai tuni hukumar gudanarwar filin ta kira taron manema labarai, tana mai shaida cewa, wa'adin shekaru 93 ne ba shekaru 40 kamar yadda ma'aikatar ƙasa ta bayyana ba.