Likitoci sun manta almakashin tiyata a cikin wata mata a Indiya
Wata mata a jihar Kerala, a kudancin Indiya da ta shafe shekaru tana fama da matsanancin zafi saboda tiyatar da aka yi mata da ba ta yi nasara ba, ta ce har yanzu tana jiran a hukunta likitocin da ke da hannu a lamarin.
Wakilin BBC Imran Qureshi ya tattauna da ita game da fafutukar da take ta neman a yi mata adalci.
KK Harshina, mai shekara 31 ta ce ta kasance tana rayuwa ne cikin matsanancin zafi a cikinta tsawon shekaru.
Sai bayan da hoton cikinta da aka É—auka a shekarar da ta gabata ya gano almakashi irin na tiyata da aka manta a cikinta.
"Ba zan iya kwatanta zafin da na É—anÉ—ana ba tsawon shekara biyar," in ji Ms Harshina.
An yi wa Ms Harshina wadda take da Æ´aÆ´a uku tiyata ne domin ciro duka jariran.
Tiyatarta ta ƙarshe kuma an yi mata ne a asibitin koyarwa na Government Medical College a 2017 inda aka ciro ɗa namiji.
Bayan tiyatar ce kuma ta soma jin raÉ—aÉ—i a cikinta, kamar yadda ta ce.
"Da na bayyana irin zafin da nake ji, likitoci sun faÉ—a min cewa ina jin haka ne saboda aikin tiyatar da aka yi min karo na uku ne," in ji ta.
"An kuma faÉ—a min cewa mata da dama suna kai irin wannan kukan."
Sai dai bayan da ta ci gaba da fuskantar zafin ta tuntuɓi likitoci da dama.