Duk wanda yace zai tada hankalin al'umma yayin gudanar da wannan zaɓe na wannan lokaci da yiwuwar ya rasa ransa domin jami'an tsaro sun shirya tsaf kamar yadda aka basu umarnin kawar da duk wanda yake da niyyar ko ya aikata wani abu da zai kawo tsaiku yayin gudanar da zabe. Amb. Ibrahim Waiya wanda ke zama shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiya ta ƙasa reshen jihar kano ya bayyana wannan batu ne yayin gabatar da wata tattaunawa ta musamman a kafar yaɗa labarai a nan kano. '' Siyasa da banbancin ra'ayi ba gaba bane kuma kar ku yarda rana ɗaya ta ɓata sauran ranaku masu muhimmanci na rayuwar ku'' inji Waiya
Mai rabon ganin baɗi ya gani ~ Amb. Ibrahim Waiya
March 18, 2023
0
Tags