Wasu mazauna birnin Kano sun yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban kasa, Sanata Bola Tinubu, da ya ba da fifiko ga tsaro da tattalin arzikin kasar nan.
Wasu daga cikin mazauna yankin da su ka zanta da manema labarai a Kano sun koka kan yadda rashin tsaro a wasu yankunan Arewa ya haifar da koma baya ga noma da kasuwanci.
Daya daga cikin mazauna yankin, Bala Shehu, manomi, wanda ya bayyana jin dadinsa da nasarar da Tinubu ya samu, ya roke shi da ya samo bakin zaren warware matsalolin tsaro a wasu yankunan Arewa a lokacin da ya karbi mulki.
Ya bayyana cewa tsoron masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ya hana manoma ziyartar gonakinsu a wasu sassan jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara.
Ya shawarci Tinubu da ya bai wa jami’an tsaro kayan aiki da kuma tallafin da suka dace don dakile miyagun laifuka a lokacin gwamnatinsa.
Wani ma’aikacin gwamnati, Mamman Sa’idu, wanda ya nuna farin cikinsa da yadda aka gudanar da zaben cikin lumana, ya bukaci Tinubu da ya yi la’akari da lafiyar jama’a da kuma daukar matakan inganta tattalin arziki.
“Ina so in yi kira gare shi da ya ba da fifiko ga tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya tare da inganta tattalin arziki,” in ji shi