Jam’iyya mai mulki, APC ta ce ta mutunta matakin da INEC ta dauka na dage zaben gwamnoni da na ƴan majalisar jiha daga ranar 11 zuwa 18 ga watan Maris.
Felix Morka, sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis a Abuja.
Ya ce dage zaben ya biyo bayan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke kan sake saita na'urar BVAS da INEC ta yi amfani da shi wajen zaben shugaban kasa.
Jam’iyyar ta ce ta lura da tabbacin da INEC ta bayar cewa za a adana bayanan da suka fito daga zaben Shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta kasa yadda ya kamata a rumbun ajiye bayanai na Umar gizo.
"Muna kira ga INEC da ta yi duk abin da za ta iya don kiyayewa tare da kare amincin bayanan da aka ciro daga BVAS kamar yadda ta kuduri aniyar yi a gaban kotu," in ji shi.
Ya kuma bukaci INEC da ta yi amfani da damar dage zaben wajen magance duk wani gibi ko cikas da aka gano a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu.