Gwamnatin Tarayya ta ce ta ta ce mutum sama da miliyan 100 sun fita daga cikin matsanancin talauci a faɗin ƙasa.
Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala'i ta Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana haka a Jalingo babban birnin jihar, yayin da ta ke wata tattaunawa da waɗanda suka ci moriyar shirye-shiryen taimakawa al'umma.
Ta ce gwamnati ta kashe naira biliyan 35.5 kan shirye-shiryen taimakawa al'umma a Jihar Taraba tun lokacin da ta ci mulki.
Ministar, wacce shugabar shirin a jihar, Beatrice Kitchina ta wakilta, dalilin wannan shiri, kuma ciki har da matasa da mata.
Ta bayyana jerin wasu shirye-shirye kamar su N-Power da CCT da GEEP ga kuma shirin ciyar da 'yan makaranta shi ma.
Sakataren shirin ciyar da 'yan makarantar Idris Goje, yace an yi maganin talauci a ƙasa da wannan shiri, haka kuma ya yi amfani a jihar Taraba.