Hukumar kare hakkin ɗan'adam ta ƙasa NHRC, ta ce ta samu akalla korafe-korafe 246 na take hakkin dan'adam daga watan Janairu zuwa Fabrairu a jihar Kano.
Ko’odinetan hukumar a Kano, Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa a yau Laraba a Kano.
Sai dai ya ce an kammala korafe-korafe 165 daga cikin 246, yayin da 81 a na aiki a kan su.
Abdullahi ya bayyana cewa, shari’o’i 174 da suka shafi mata da matsalar jinsi, 17 kuma sun shafi ƴancin jama’a da siyasa, kamawa da tsarewa ba bisa ka’ida ba.
Ko’odinetan ya kara da cewa 45 daga cikin kararrakin da aka samu a tsawon lokacin da ake bitar sun hada da watsi da ayyukan iyali, rikicin cikin gida da kuma fyade.
"Sauran shari'o'in guda 10 sun shafi yara, aiki da dai sauransu," in ji Abdullahi.
Ya bayyana cewa hukumar ta kuma shiga tsakani kan harkokin aure tsakanin ma’aurata da iyalai.
Malam Abdullahi ya bukaci ma’aurata su kara hakuri da juna domin samun zuriya mai inganci .