Wata kungiyar rajin kare dimokradiyya ta kasa, NADECO, ta bukaci hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, da ta damke wasu mutane da ke da niyyar kawo cikas ga mulkin dimokuradiyya na mika mulki daga shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Sen. Bola Tinubu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Atilade Adeeyo ya fitar a Oye-Ekiti.
“Mu na kira ga hukumar ta DSS da ta kawo karshen ayyukan rashin demokradiyya da rashin kishin kasa da ke kokarin kawo cikas ga tsarin mulkin dimokuradiyya daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa ga zababben shugaban kasa.
“Al’ummar kasar nan ta shaida yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa cikin kwanciyar hankali, adalci da walwala da sauran wadanda suka haifar da sabbin shugabannin da za su gudanar da harkokin siyasa na gaba a kasar nan.
“Wasu makiyan al’umma ba za su bari zaman lafiya ya yi mulki ba saboda son kai da kwadayin mulki.
“Kada mu bari wasu masu son kai, mara sa kishin kasa da rashin kishin kasa wadanda su ke fifita son zuciya sama da muradun jama’a da kishin kasa su kawo cikas ga wannan tsarin mika mulki tare da jefa al’ummar mu cikin rudani,” in ji kungiyar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, hukumar ta DSS a ranar Laraba ta ce ta tabbatar da makircin da wasu 'yan siyasa ke yi na kafa gwamnatin riko a Nijeriya.
Sai dai kuma mai magana da yawun hukumar DSS ɗin, Peter Afunanya a wata sanarwa da ya fitar, hukumar ta ce ta gano wadanda ke da hannu a wannan makircin da ke kawo cikas ga dimokuradiyya bayan babban zaben 2023.