Lokacin da Kwankwaso ya karɓi jihar kano a shekarar 2003 babu abunda bai yi ba don ganin ya kawar da zaluncin manya da kuma dakatar da rainin da akewa kujerar ta gwamna tare da amfani da kima ta masarautu don zaluntar al'umma wajen danne musu haƙƙunan su da mallakwa wanda suke so dukiyar duk wanda suka ga dama, wannan al'amari ne yasa wasu manyan garin marasa kishin ƙasa suka ƙirƙiri wata tsana ta musamman suka ƙaƙaba masa tare da amfani da ɗabi'ar mutanen kano ta girmama manya da duk wani abu da suka zo dashi akai amfani da wannan don nunawa al'umma cewa Kwankwaso ba mutumin kirki bane kuma baya girmama manya da muradan su, hakan ba karamar illa ya yiwa siyasar shi ba kuma mutane a gefe guda saka tsane shi dashi das duk wasu masu son shi sai da sukai duk mai yiwuwa wajen kawar da gwamnatin sa domin bayan da akai zaɓe an kada shi kuma cikin ikon Allah ya yarda aan kada shi ya kuma bayar da kaddara ya bayar duk da yana da damar sawa a murɗe masa zaɓen a lokacin. Koda Kwankwaso ya sauka sai da zaman kano ya gagare shi domin duk inda ya nuna kansa sai an jefe shi sai dai idan ɓoye fuskar sa yayi.
Kwankwaso ya dawo da ƙarfin dimokaraɗiyya tare da kudiri kyakykyawa a zuciyar sa wanda yaƙi fitowa dashi don ko a wajen kamfen ɗinsa ba fada ba a shekarar 2011. Akai duk mai yiwuwa a ƙarshe dai Allah ya mallaka masa kano ya dora a kan abunda yayi a baya na kin baiwa manyan gari damar take hakkin talaka tare da ɗaukar nauyin ƴaƴan talakawa izuwa kasashen ƙetare da baiwa wasun su jari a gida domin dogaro da kansu wanda har izuwa yanzu wasun su na amfana da wannan jari su kuwa waɗanda sukai karatu ba'a maganar su domin sun zama ababen kwatance a duniya. Lokacin daya sauka sai ya miƙa mulki ga mataimakin sa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ofr kamar yadda manya a jam'iyyar suka bukata shekaru biyu da karɓa ya canza akalar shirye-shiryen daya kafa gwamnatin a kai, a ƙarshe akai baran-baran aka kasa gane mara gaskiya tsakanin su domin kowannen su ya bada hujjoji kuma an gamsu sai dai daga baya an gano cewa GANDUJE shine wanda baida gaskiya shi yasa da yace mutane kar su zaɓe shi suka kada shi a shekarar 2019 amma aka ƙwatar masa mulkin saboda kudirin da jam'iyyar APC keda shi a zaɓen 2023 na shugabancin ƙasa. Ta tabbata cewa Kwankwaso yaci kano amma an hana shi kamar yadda ake zargi. Ya dawo a shekarar 2023 inda ya nemi zama shugaaban kasa ƙarƙashin tutar sabuwar jam'iyyar NNPP kuma yai Nasara a iya kano inda ya samu ƙuri'un ds suka gaza dubu ɗari tara wanda babu wani ɗantakara na shugabancin ƙasa daya samu irin kuri'ar sa a jihar sa. Haka shima Abba Kabir Yusuf inda ta nuna shi kuma aka zaɓe shi kamar dai yadda Kwankwaso ya bukaci al'umma suyi.
Nan gaba bayan ABBA ya kammala mulki Kwankwaso bashi da buri daya wuce ya tallafawa matasan jihar kano su zama sune masu mulki a jihar kuma kamar yadda a yanzu zai saka Abba ya naɗa matasa a matsayin kwamishinoni a jihar kano, manyan da suke taimakawa tafiyar su kuma a dunga basu kwangiloli na gina jiha. Shi yasa idan har ya karɓi jihar kano a yanzu babu yadda za'ayi nan da shekaru 50 a karbe ta domin masu tasowa su ake baiwa dama.