Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta bayyana gwamnan jihar Oyo kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Seyi Makinde, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar.
Hukumar zabe ta jihar INEC, Tella Adeniran, ta bayyana Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben a yau Lahadi.
Yayin da Makinde ya samu kuri’u dubu 563,756, abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Teslim Folarin ya samu kuri’u dubu 256,685.
Ya kuma yi nasara a kananan hukumomi 31 daga cikin 33 na jihar.