Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama wasu mutane 50 da ake zargi da yin sace-sace a kasuwar Monday Market ta Maiduguri jihar Borno.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Kamilu Shatambay ya tabbatar da kama wadanda ake zargin a ranar Laraba a Maiduguri.
Ya ce jami’an rundunar da aka tura domin kare rayuka da dukiyoyin da gobarar ta afku a kasuwar, sun kama wadanda ake zargin ne a ranar 26 ga watan Fabrairu.
Ya ce wadanda ake zargin sun yi awon gaba da kadarorin wadanda abin ya shafa a lokacin da ‘yan kwana-kwana da jami’an tsaro ke fafutukar kashe gobarar.
Kakakin ya ce rundunar ta kuma kama wani mutum mai suna Sadiq Ibrahim mai shekaru 20 da laifin kona wata motar rundunar hadin gwiwa ta CJTF.
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
A cewarsa, kwamishinan ‘yan sanda, Mista Abdu Umar ya jajantawa gwamnatin jihar tare da yin kira ga wadanda abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu domin gwamnati na yin duk mai yiwuwa don rage radadin da suke ciki.