Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta samu Karin Sabbin kayan aiki Domin tunkarar zaɓen
Gwamna dana Yan Majalissu da zaa gudanar a Ranar Asabar Mai zuwa.
A wani Sako daya aikawa manema labarai Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewar, sun samu Karin kayan ne daga babbar headquartar hukumar Yan Sanda Dake Abuja, Kuma wadannan kayan aikin zasu taimaka musu wajen tafiyar da aikin zaɓen lami Lafiya.