Sifeto-Janar ya soke kawo CP Olaleye, ya aiko Kontagora a matsayin sabon Kwamishinan Ƴansanda zuwa Kano
Sufeto Janar, IGP Alkali Baba ya soke turo da Feleye Olaleye a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda a Kano.
A don haka, IGP din ya aiko CP Ahmed Kontagora ya jagoranci rundunar a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a jihar.
A ranar 8 ga Maris, IGP ya sauya matakin da ya dauka na tura CP Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaro na gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, biyo bayan zanga-zangar da aka yi a kan hakan.
Amma a wata sigina da aka fitar ranar Litinin mai lamba TH.5361/FS/FHQ/ABJ/SUB.6/144, IGP din ya ci gaba da tura CP Ita Lazarus Uko-Udom zuwa Kano ta Tsakiya, inda DCP Umar Iya ya zama mataimakin sa.
Yanzu haka dai IGP din ya mayar da CP Faleye Olaleye daga jihar Ebonyi zuwa Kano domin ya jagoranci rundunar a lokacin zabe.
Jam'iyyar adawa ta NNPP ta gudanar da zanga-zanga bayan rahoton DAILY NIGERIAN na cewa za a turo mutane uku, CP Balarabe Sule, ACP Adamu Babayo da ACP Abubakar Shika zuwa jihar Kano
A cewar masu lura da al’amura, ‘yan sandan uku, wadanda suka taba yin aiki tare a jihar, ana kyautata zaton jami’an bangaranci ne da ake amfani da su a matsayin jami’an murkushe ‘yan adawa.
Shafin Raihana dai ta tattaro cewa zanga-zangar ta yi tasiri ga IGP ɗin inda ya fasa aiko CP Sule ɗin.
IGP din ya kuma sake tura karin wasu manyan jami’ai zuwa jihar domin karfafa tsaro a lokacin zabe.
Kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta gani na baya-bayan nan, IGP din ya tura AIG Sani Dalijan domin ya jagoranci shiyya ta daya a Kano.
Haka kuma takardar ta nuna cewa Ita Lazarus Uko-Udom ne zai jagoranci Kano ta tsakiya, inda DCP Umar Iya zai kasance na biyu a matsayin shugaba.
Alkali ya kuma aike da DCP Abdulkadir El-Jamel domin kula da kananan hukumomin Albasu, Gaya, Rogo, Takai, Ajingi, Garko, Wudil da Sumaila.
A kananan hukumomin Rano, Bebeji, Bunkure, Doguwa, Kiru, Kibiya Tudunwada dake jihar Kano ta kudu kuwa, IGP ya tura DCP Adamu Ngojin domin ya kula da tsaron a can haka.
IGP din ya kuma tura DCP Abaniwonda Olufemi zuwa Kano ta Arewa, tare da ACP Adamu Sambo a matsayin babban kwamandan sa na biyu.
Kamar yadda sabuwar takardar ta nuna, DCP Auwal Musa ne zai jagoranci CID, yayin da DCP Aminu Maiwada zai dauki nauyin gudanar da ayyuka a hukumar ta Kano a lokacin zabe.