Jihar Sokoto Maris 21, 2023
SANARWA
Ana sanar da al'ummar musulmi cewa ranar Laraba 22 ga watan Maris 2023 daidai da 29 ga watan Sha'aban 1444AH ta zama ranar neman jinjirin watan Ramadan 1444AH.
Don haka ake kira ga al’ummar musulmi da su fara duban jinjirin watan Ramadan 1444AH a gobe Laraba, sannan su kai rahoto ga Hakimi ko Kauye mafi kusa don tuntubar mai martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, mni, Sarkin Musulmi. .
Allah (SWT) Ya taimake mu wajen sauke wannan aiki na addini.
Prof. Sambo Wali Junaidu
Wazirin Sokoto Shugaban Kwamitin Ba da Shawara Kan Al'amuran Addini, Majalisar Sarkin Musulmi, Sokoto