Hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta Saudiyya ta yi kira ga masu ziyarar ibada zuwa wurare masu alfarma da su martaba darajar wuraren.
Sannan kuma ta gargade su da su bi dokoki wajen ɗaukar hotunan a wurare masu tsarki.
Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su ɓige da ɗaukar hotuna, a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su ƙasa mai tsarkin.
Haka kuma hukumar ta gargaɗi masu ɗaukar hotunan da su guji haɗawa da wasu mutanen a cikin hoton nasu, ba tare da izini ba.
Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don ɗaukar hoto a wuraren da jama'a da dama suka taru, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama'a a wuraren.
A baya-bayan nan dai mutane sun ɓullo da salon ɗaukar hotuna a lokacin ziyarar ibada zuwa ƙasa mai tsarkin tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta.
Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa zai iya zama 'Riya', abin da kuma a cewar malaman zai iya ɓata wa mutanen ibadar tasu.