Shafin Raihana ya rawaito cewa Murja ta shafe makonni uku a gidan yari bayan Æ´an sanda sun cafke ta sun kuma gurfanar da ita a kotu.
Kotun dai na tuhumar Murja da laifuka da su ka shafi yarfe, ashariya, gurÉ“ata tarbiyya da yunÆ™urin tada hankalin al’umma.
Hakazalika kotun, a makonni biyu da suka gabata, ta gurfanar da abokan Murja na TikTok su uku, sa su ka haÉ—a da Aminu Ibrahim, mai lakabin BBC, Ashiru Idris Maiwushirya da kuma Sadiq Sharif, inda ta aike su gidan yari tare da ita.
Sai dai kuma da ya ke yanke hukunci a jiya, alÆ™alin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Halliru ne ya yanke wa Murja hukuncin sharar makeken asibitin Murtala.
Sannan kuma za ta riƙa zuwa hukumar Hisbah ta jiha har tsawon watanni shida.
Haka suma, BBC, Maiwushirya da Sadiq Sharif, an yanke musu hukuncin sharar asibitin Murtala bisa kama su da laifin yaɗa batsa da yunkurin gurɓata tarbiyya, inda duk su ka amsa laifukan su.
Lauyan Zauren Malamai na jihar Kano, Badamasi Gandu, wanda su ne su ka shigar da korafi tun da fari, ya ce yanzu haka ana neman sauran Æ´an TikTok É—in irin su Ado Gwanja, Ummi Shakira da 442, wanda ya ke tsare a Nijar, inda ya ce su ma za a hukunta su idan an kama su