Dokta Sodipo Oluwajimi, kwararre a kan cin zarafin mata da maza, GBV, kuma Likitan Iyali a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Legas, Ikeja, ya ce su ma yara maza na fuskantar cin zarafi a kasar nan.
Oluwajimi ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Ilorin a jiya Juma’a.
Ya yi magana ne a kan taron horo da aka shirya wa likitoci karkashin shirin 'Stand Up Against Rape Initiative.'
A cewarsa, yara maza su ma su na fuskantar fyade, luwadi da kuma lalata da su a kasar nan.
Ya ce: "Ba ƴan mata ko mata kadai ke fuskantar GBV ba.
"Mata da maza duka suna fuskantar tashin hankali irin wannan amma yawancin wadanda abin ya fi shafa su ne mata da ƴan mata.
"GBV da cin zarafin mata kalmomi ne da ake amfani da su akai-akai kamar yadda aka yarda da cewa yawancin cin zarafin a kan mata da 'yan mata ne," in ji shi.