Sabon zaɓabben shugaban Najeriya mai jiran-gado Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya aika da saƙon jaje ga ƴan kasuwar da suka yi asarar dukiyarsa da gobara ta ci a jihar kano
A wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar a yau Talata, wadda ke ɗauke da sa hannun Abdulaziz Abdulaziz, Tinubu ya nuna takaicinsa kan bala'in gobarar da ya afka wa wani sashe na kasuwar Singer da kuma wasu kasuwannin biyu (Kurmi da Rimi) a jihar, duka a 'yan kwanakin nan.
Ya ce ya kaɗu da jin irin ɓarnar da bala'in ya haddasa ga al'ummar Kano da ma gwamnatin jihar.
Sannan ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su yi ƙoƙarin gano musabbabin tashin gobarar da ake ta samu a sassan Najeriya, tare da agaza wa waɗanda suka yi asara.