Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya bukaci zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da ya hada tawagar da ta kunshi masana da kwararru domin fito da kundin tsarin farfado da tattalin arzikin Nijeriya.
Ooni ya yi wannan kiran ne a cikin sakon taya murna ga zababben shugaban kasa Bola Tinubu, mai dauke da sa hannun Otunba Moses Olafare, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a fadar da ke Ile-Ife, jihar Osun.
"Dole ne ku gaggauta hada tawagar maza da mata don samar da tsarin farfado da tattalin arziki a yayin rantsar da ku a ranar 29 ga Mayu.
“Dole ne ku matsa kaimi ta hanyar da za ta kara tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa taken 'Sabuwar rayuwa' ɗin nan mai tabbatuwa ne.
“A matsayin wanda aka gwada kuma amintaccen shugaba, dole ne nan da kwanaki kaɗan ka gabatar da ƙungiyar canjin ku ta maza da mata don ba mu tsarin farfado da tattalin arziki.
"'Yan Najeriya sun zabe ku ne saboda alkawarin da kuka yi na sabbin kudure-kudure kuma dole ne ku gaggauta daga ranar farko da kuka fara aiki a kan karagar mulki ta hanyar da za ta kara tabbatar wa 'yan Najeriya "Sabuwar rayuwa", in ji Ooni.