Wata likita mai suna Maria Fadaka, a ranar Litinin ta shaida wa kotu a Ikeja, yadda wani Fasto mai suna Chris Mcdouglas, ya yi lalata da wata ‘yar wata mamba ta cocin sa mai shekaru 17.
Mcdouglas, wani Fasto a Cocin Peculiar Generation Assembly, Legas, yana fuskantar tuhume-tuhume tara da su ka hada da lalata da kuma lalata matancin yarinya.
Sai dai ya musanta aikata laifin.
Fadaka, jami'ar kula da lafiyar jama'a ce a Mirabel Medical Centre, (cibiyar da ke duba waɗanda aka yi wa fyaɗe), a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Legas, LASUTH.
Darekta mai shigar da kara na jihar, Dr. Babajide Martins ne ya kai ta gaban kotu.
Likitan ta shaida wa kotu cewa wacce aka yi wa fyaɗen, (an sakaya sunanta) ta gabatar da kanta don duba lafiyarta a ranar 12 ga Mayu, 2020, mako guda bayan da aka yi zargin yin lalata da wanda ake kara na karshe.
A cewarta, “Wacce akai wa fyaɗen ta zo Cibiyar Mirabel a ranar 12 ga Mayu, 2020 kuma ta koka da cewa fyade da Fasto ya yi mata.
“ta kara da cewa jima’i na karshe da faston ya yi da ita ya faru ne kusan wata guda kafin gabatar da ita ga cibiyar.
"Sakamakon gwajin likita ya nuna cewa faston ya yi amfani da karfi wajen yin lalata da yarinyar," in ji ta.