Dzukogi, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a jiya Laraba, ya ce lamarin na baya-bayan nan shi ne na biyu cikin jerin hare-haren wariyar launin fata da ‘yan sanda suka kai masa.
Dzukogi, wanda mataimakin farfesa ne a Jami’ar Jihar Mississippi, duk da haka, ya nuna godiya ga Allah cewa ya tsallake hare-haren ba tare da lafiyarsa ta taɓu ba.
Ya rubuta cewa, “Wannan shi ne karo na biyu a wannan shekara da ƴansanda a Mississippi ke cin zarafi ma ba tare da wani dalili ba sai don kawai ni bakar fata ne.
“Na farko, yayin da nake yawo a unguwarmu sanye da kayan bacci, sai kuma a a yau, a na je ganin wani likita. Na gode dai ina cikin koshin lafiya kuma rayuwata har yanzu tawa ce.