Akalla Musulmai 1000 ne marasa galihu a yau Laraba, suka amfana da kayan abinci da kudi daga wata Coci da ke Kaduna gabanin fara azumin kwanaki 30 na watan Ramadan a gobe Alhamis.
Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry da ke Sabon Tasha Kaduna ce ta bayar da gudummawar buhunan hatsi da tsabar kudi a babban masallacin Juma’a na Kano Road da ke Kaduna.
Da ya ke mika kayayyakin ga wadanda suka ci gajiyar, babban mai kula da cocin, Fasto Yohanna Buru, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin karfafa hadin kai, zaman lafiya da zumunci a tsakanin mabiya addinan biyu.
Buru ya ce hakan ya kuma zama wajibi musamman a wannan lokaci da ƴan Nijeriya da dama ke fama da matsalar karancin kudi da hauhawar farashin man fetur.
Ya ce a shekarar da ta gabata cocin ta ba da tallafin buhunan shinkafa da masara da sauran kayan abinci ga al’ummar Musulmi marasa galihu a jihohi sama da biyar a cikin watan Ramadan.
Ya kara da cewa a bana sun kara da dardumai da burodi domin yin Sallah da addu'o'i ga Ubangiji.