Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben Kano da za a yi ranar Asabar, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce kamata ya yi hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana zaben bai kammalu ba.
Dan takarar gwamnan wanda ke tare da shugabannin jam’iyyar, ya bayyana mamakinsa cewa da zaben daya gudana, zabukan ‘yan majalisun tarayya guda 16 da aka gudanar a rana guda kuma hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa ba a kammala ba.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa INEC da safiyar ranar Litinin ta bayyana Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar ranar Asabar.
Hakazalika, jam’iyyar APC ta yi watsi da sanarwar Abba Kabir Yusif na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka kammala a Kano inda ya bukaci INEC ta gaggauta sake duba sakamakon zaben cikin kwanaki bakwai.
Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas ne ya sanar da hakan ga manema labarai a wani taron gaggawa da ya yi da manema labarai a ofishin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a Kano, ranar Talata.
Shugaban jam’iyyar APC, wanda ya samu wakilcin mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Abdul Adamu Fagge, ya dage cewa ya kamata a ce zaben bai kammala ba saboda kuri’un da aka soke sun fi tazarar da ke tsakanin jam’iyyun NNPP da APC na daya da na biyu kamar yadda dokar zabe ta tanada.
Jam’iyyar ta kuma ja hankali kan soke zaben ‘yan majalisar dokoki goma sha shida da aka yi a jihar, inda ta ga tashin hankali a matsayin dalilin, yayin da aka yi la’akari da kuri’u guda wajen tattara zaben gwamna. Ya nuna rashin jin dadinsa yana mai cewa zabukan biyu sun gudana a rana guda, lokaci guda, wurare guda da kuma yanayi iri daya.