Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta ce, ta gano shirin wasu Ƴansiyasa na shigo da ƴandaba jihar don tada hargitsi a lokacin zaɓe.
Rundunar ta gargaɗi ƴan siyasar da su dakatar da wannan yunƙuri domin gudun faɗa wa hannunta.
Ƴansandan sun ce, duk wanda aka samu da hannu a tarzoma zai ɗanɗana kuɗarsa.
Rundunar ta kuma nemi jama'a da su gaggauta sanar da jami'anta duk inda suka ga baƙin fuska.
Daga Jaridar Raihana