Hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wadda ya lashe zaɓen da adadin ƙuri’u 8,794,726, tazarar ƙuri’a kusan miliyan biyu tsakaninsa da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
Atiku mai shekara 76, ya samu ƙuri’a 6,984,520, yayin da Peter Obi na LP – wanda a ƙasa da shekara guda ya tara matasan mabiya- ya bayar da mamaki a takarar inda ya samu ƙuri’a 6,101,533.
To sai dai Atiku da Obi dukkansu sun yi zargin maguɗi a zaɓen, inda suka sha alwashin ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu.
A wata sanarwa da Amurkan da fitar ta hannun jakadiyar ƙasar a Najeriya Mary Beth Leonard, ta ce ‘yan Najeriya da dama sun fusata game da sakamakon, inda wasu suka riƙa murna kan nasarar da suka samu.
Sanarwar ta ƙara da cewa “A bayyane take cewa tsarin zaɓen Najeriya da aka gudanarar ranar 25 ga watan Fabrairu ya gaza cimma yadda ‘yan ƙasar suka yi tsammani,”
“Kamar yadda na sha faɗa a baya gabanin zaɓen, Najeriya ta cimma abubuwa masu yawa a tsawon shekaru sama da 20 da ta yi bayan komawa tafarkin dimoraɗiyya, kuma ci gaban da aka samu a fannin zaɓukan ƙasar na daga cikin nasarorin da ƙasar ta cimma”
“Yan Najeriya sun nuna sadaukarwarsu ga dimokraɗiyya ranar 25 ga watan fabrairu, to sai dai da yawa sun nuna fusata, yayin da wasu da dama suka nuna murna bayan nasarar da suka samu”.