Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar Musulmi da sauran al’ummar Kano murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma bukukuwan Sallah karama.
A wata sanarwa da kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a yau Juma’a, Yusuf ya kuma bukaci mazauna jihar da su dore da aiwatar da darussa da tarbiyyar da’a da suka koya a cikin watan Ramadan.
Ya ce” Ramadan ya zo karshe da ganin jinjirin watan Shawwal, darussa na tausayi, karimci, tarbiyya, kishin kasa da zaman lafiya da ya kamata yan kasa su dore da shi don samun al’ummar da ta dace.”
Yayin da ya ke taya al’ummar Musulmi murnar sake shedar Idil-Fitr, Mista Yusuf ya bukaci al’ummar Kano da su yi addu’ar Allah ya ba su shugabanni na gari a dukkan matakai musamman yadda sabuwar gwamnati za ta karbi ragamar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.Ya ba da tabbacin cewa kwanaki masu kyau na gaban mutanen Kano domin gwamnati mai jiran gado a karkashin sa za ta samar da yanayi mai kyau ga kowa ya zauna lafiya da kwanciyar hankali.
“Ya bukaci ‘yan kasa da su kasance masu kishin kasa, masu son zaman lafiya tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban Kano da Nijeriya baki daya.
“H.E. Abba Kabir Yusuf ya kuma yi gargadi game da tukin ganganci a yayin bukukuwan Sallah da kuma gujewa abubuwan da za su haifar da rashin tsaro da nufin tabbatar da tsaron daukacin mazauna Kano,” in ji sanarwar.