Smiles Africa International Youth Development Initiative, SAIYDI,
wata ƙungiya mai zaman kanta ta bayar da shawarar a yi garambawul a dokokin da suka haramta amfani da miyagun kwayoyi masu tsauri don masu yi don nishaɗi a Nijeriya.
Purpose Iserhienrhien, Babban Darakta, SAIYDI, ne ya bayar da shawarar hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Benin.
Iserhienrhien, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na NAN a wani shiri na tsawon kwanaki uku ga masu amfani da muggan kwayoyi, PWUD, ya ce kamata ya yi gwamnati ta riƙa kyale magungunan da ake sha don nishaɗi ga masu ta’ammali da su.
Ya bayyana cewa akwai bukatar dokar da ta haramta amfani da wasu kwayoyia sake duba a cikin ta don masu sha domin nishadi.
“Idan a ka samu bayanan da suka dace game da magani, to kada a riƙa kaucewa ka’idojin amfani da shi. Ya kamata a bar mutane su sha kwayoyi don samun nishaɗi.
“Mutane na shan kwayoyi na nishaɗi don ƙara ƙarfin jima’i, don jin daɗi da ƙarin kuzari; duk wanda ke shan ƙwayoyi don wannan dalilin to bai aikata laifi ba,” in ji shi