Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya ce ba zai yiwu Aisha Binani ta jam’iyyar APC ta zama gwamnan jihar Adamawa ba.
Lawal yayi ikirarin cewa Binani ba ta cancanci zama gwamnan Adamawa ba, ya kara da cewa ba ta da halayen wannan mukami kuma bata samu kuri’un da ake bukata ba a zaben gwamna na farko da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, tsohon SGF ya ce: “Allah Ya kiyaye, ba zai yiwu Binani ta zama gwamnan jihar Adamawa ba.
“A farko dai ba ta cancanta ba, bata da hali kuma bata samu kuri’u ba, a lokacin zaben farko ku lura ni ba PDP ko APC nake ba''.
“Amma PDP ta samu kuri’u 421525 ita kuma APC ta samu kuri’u 380275, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri’u sama da 31,000 a wancan mataki, yanzu bayan hada kananan hukumomi 20 daga cikin 21 da ke Adamawa saura karamar hukuma daya ta rage, kuma hakan ya sa aka samu kuri’u fiye da 31,000. shine inda matsalar ta faro.
"Sun fara tantance sakamakon, sun saci sakamakon sannan suka fara sarrafa shi."
Wannan ikirari na Lawal ya biyo bayan cece-kucen daya biyo bayan tattara sakamakon zaben da aka yi a jihar ranar Asabar.
Kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, ya tayar da tarzoma bayan ya bayyana Binani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben.
Kafin a dakatar da taron tattara sakamakon zaben a daren ranar Asabar, an bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi goma inda Binani ke biye da gwamna mai ci kuma dan takarar PDP, Ahmadu Fintiri.Sai dai INEC ta yi gaggawar yin tir da sanarwar da aka ce ta kuma dakatar da tattara sakamakon zaben da aka kara.
Alkalan zaben ya kara sammaci REC zuwa Abuja ba tare da bata lokaci ba.