An yi garkuwa da wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun, TRACE, Popoola Olasupo a jiya Lahadi a hanyar Fidiwo da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya tattaro cewa an yi garkuwa da Olasupo ne da misalin karfe 6:30 na safe a lokacin da ya ke tafiya wajen aiki.
An kuma tattaro cewa ƴansanda da ƴan vigilante na kan hanyarsu ta neman garkuwa da mutanen.
A cewar wani ganau, kwatsam masu garkuwar sun fito daga cikin daji inda suka bude wuta kan wata motar bas ta haya da nufin yin garkuwa da mutanen da ke ciki.
Daga karshe dai babu daya daga cikin fasinjojin da aka sace, sai jami'in TRACE yayi rashin sa'a an tafi da shi.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yansandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta, inda ya ce tuni rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane a jihar ta bi sahun masu garkuwa da mutanen.
“Rundunar mu ta yaki da garkuwa da mutane tuni ta bi su, muna tafe dazuzzuka kuma mun san za a kama su duka.
“Jihar Ogun ba wurin da masu laifi za su sakata su wala ba ce. Ko dai su fita ne ko kuma mu fitar da su daga wannan jihar,” inji shi.