Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da wani jami'in tsaron gida yari mai suna mista Eyimoga Moses a gaban Babbar Kotun Tarayya a Makurdi, babban birnin jihar Benue, inda take zarginsa da sayar da aiki.
BBC ta rawaito cewa ICPC ta ce tana zargin Moses wanda ke aiki a gidan yari da ke jihar Nasarawa da laifin karɓar 800,000 daga hannun wasu ma'aurata da karyar cewa zai sama musu aiki a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia.
Sai dai Moses ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, inda aka bayar da belinsa yayin da ake ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali a Makurdi har sai ya cika sharuɗan belinsa da aka bayar.
An ɗage zaman kotun har sai 20 ga watan Yunin 2023 domin ci gaba da sauraron shari'ar.