Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 cikin gaggawa a yankin Sabon Garin Nassarawa-Tirkaniya a karamar hukumar Chikun.
Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.
Ya ce an cimma matsayar ne biyo bayan tabarbarewar doka da oda da ta kai ga kashe wasu mutane guda biyu a wani rikici da ya barke a garuruwan yankin.
“An umurci hukumomin tsaro da su aiwatar da dokar hana fita a wurin da aka ce, don dawo da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da bincike. Don haka an yi kira ga mazauna yankin da su kiyaye dokar hana fita a wannan wuri, wanda za ta fara aiki nan take.
"Za a sanar da ƙarin sabunta dokar idan lokaci ya yi," in ji Aruwan.