Rundunar ƴansandan jihar Enugu ta kama wasu mata biyu da suka shahara wajen sata da siyar da yara kanana a jihar.
Premium Times Hausa ta rawaito cewa Kakakin rundunar Daniel Ndukwe ya ce rundunar ta kama Miracle Orji mai shekara 24 da Blessing Ani mai shekara 34 a cikin makon jiya.
Ndukwe ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya taimaka wajen ceto wani yaro karami da Miracle ta sace ranar 24 ga Maris.
Ya ce jami’an tsaro sun kama Miracle a kauyen Ameke-Oduma dake karamar hukumar Aninri yayin da take kokarin guduwa da yaron da ta sace.“Bayanin da Miracle ta yi wa jami’an tsaro ya taimaka wajen kamo abokiyar aikinta Blessing Ani.
“Jami’an tsaro sun cafke Blessing a kantin Shoprite yayin da take jiran Miracle ta zo da yaron domin ta siyar wa kwastoman su.
“Kama wadannan mata ya taimaka wajen ceto wani yaro mai shekara daya da suka siyar wa wani a Abuja.
“Blessing ta ce tun a shekarar 2021 take sana’ar satan ‘ya’yan mutane tana saidawa.
Ndukwe ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran mutanen da suke aiki tare sannan da zaran sun kammala bincike za su kai mutanen kotu domin a yanke musu hukunci.