Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun tabbatar da kama mambobin kungiyar ƴan shi'a 19 kan gudanar da zanga-zanga ba tare da izini ba.
BBC Hausa ta rawaito cewa a wata sanarwa da ta samu a hannun mai magana da yawun ƴan sandan, SP Josephine Adeh, ta ce mambobin kungiyar sama da 400 sun fito zanga-zanga daga Babbar Kotun Tarayya zuwa dandalin Eagle Square.
Sanarwar ta ce bayan fitowarsu sun kuma toshe hanyoyi bayan hukuncin da kotu ta yanke na yin watsi da bukatar bai wa jagoran kugiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky fasfo din sa.
El-Zakzaky ne ya shigar da ƙarar Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, inda ya bukaci ta sake masa fasfo ɗin sa da na matarsa da ta ƙwace.
Sai dai da yake yanke hukunci, mai shari'a Obiora Egwuatu, ya ce El-zakzaky ya kasa gabatar da hujjoji da suka nuna cewa DSS ɗin ta karɓe masa fasfo bayan dawowarsa daga Indiya.
Josephine ta ce mmbobin kungiyar sun yi ta jifar duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari kan ƴan sanda, amma daga bisani aka samu damar tarwasa su tare da kama 19 daga ciki waɗanda ta ce za a kai su kotu.