Sai dai kuma Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, ya ce a matsayinsa na dan jihar, zai rika baiwa gwamnati shawarwari masu ma’ana idan an nema.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP É—in ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa a lokacin da yake mayar da martani game da fargaba da wasu ‘yan Najeriya suka nuna cewa ba zai bari sabon gwamnan ya tafiyar da gwamnatinsa ba salin-alin ba.
Sai dai kuma Kwankwaso ya nuna cewa zai yi adawa da sabuwar gwamnatin a duk lokacin da ta kauce daga muradun al’umma.
Ya ce, “Ko da mai goge-goge ka nada a matsayin shugaba, to kada ka tsoma masa baki. Idan ya nemi shawarar ka, za ka ba da ita; idan bai tambaya ba to ka yi shiru.
“Lokacin da na ke gwamna, na yi aiki da wasu mutane ciki har da Abba, wadanda suka taimaka min wajen samun nasara.
“Don haka ne muka zauna muka kalli mutanenmu gaba daya, muka zabi wanda muke tunanin idan Allah ya kaimu, ba zai yi mana irin abinda Ganduje ya yiba.
“Duk wanda ke mulkin Kano, ko soja ne ko wanene, ba za mu bar shi ya kauce hanya ba.
“Don haka ko Abba ne, ko wanene, za mu gaya masa duk abin da ya dace, inda kuma aka yi ba daidai ba, nan ma za mu gaya masa.
“Abin da na sani shi ne cewa za a gyara duk kura-kuran da gwamnati mai barin gado ta tafka,” in ji Kwankwaso.