Tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, ya shawarci ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, da ya janye karar da ya shigar na kalubalantar zaben Bola Ahmed Tinubu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.
Nnamani ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Abuja, inda ya bukaci Obi da magoya bayansa da su amince da gaskiyar cewa Tinubu ya zama zababben shugaban ƙasa.
“Obi ya san ba shi da magoya baya a fadin ƙasar nan, abin da Obi ke kokarin yi na shigar da karar nan wani salo ne na rage wa Tinubu farin jini.
"Ƙarar nan da Obi ya shigar na inda za ta je. Shi bai karbu a fadin ƙasar nan ba. Kawai dai ya shigar da kara domin ya ragewa Tinubu farin jini ya kuma bata masa suna.
"Kokarin da ya yi na bayyana batutuwan da ba na zabe ba kawai dai wani salo ne na kokarin kunyata zababben shugaban kasa," in ji shi