Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce Kwamishinan Zabe, REC, na Adamawa da aka dakatar, Yunusa Ari, ya yi ɓatan-dabo.
Kakakin hukumar ta INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a jiya Juma’a.
A cewar Mista Okoye, REC din ya ƙi ya daga kiran da ake ta yi masa a waya, sannan ya ƙi amsa gayyatar da aka aika masa ya bayyana a shelkwatar hukumar.
Ya ce: “Ba mu san inda yake ba, domin bayan faruwar wannan lamari, hukumar ta rubuta masa takarda kuma ta kira shi a waya. Ko daya daga ciki bai aiwatar ba, bai amsa wayar ba bai kuma amsa gayyatar ba.
“Mun tambaye shi ya je hukumar ranar Lahadi, ba mu gan shi ba; mun nemi ya je ranar Litinin, ba mu gan shi ba. Don haka har ya zuwa yanzu, bai zo ba, kuma ba mu san inda yake ba.”
Da aka tambaye shi ko hukumar za ta bayyana neman sa a matsayin ruwa a kallo, Mista Okoye ya ce hakan yana ƙarƙashin ikon rundunar yansandan Najeriya.