Abba Yusuf, a wata sanarwa da kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a yau Asabar ya ce duk hukuma ko ma’aikatar da ta baiwa gwamnatin Kano mai barin gado bashi daga ranar 18 ga watan Maris to ta É—auki asara domin gwamnatin shi, idan an rantsar da ita, ba za ta biya bashin ba.
A tuna cewa a ranar Alhamis, zaɓaɓɓen gwamnan ya baiwa masu gine-gine a filayen gwamnati shawarar da su dakata.