Wannan dai ya zo ne bayan fitar da wani rahoton da ke ɗauke da farashin masu amfani da kayayyaki na watan Maris na shekarar 2023 a Abuja ranar Litinin.
NBS ta ce a kowace shekara, ana yawan samun hauhawar farashin kayayyaki a watan Maris, inda a wannan shekara ya kai kashi 6.13 bisa ɗari fiye da yadda aka samu a watan Maris ɗin 2022 wanda yake a kashi 15.92 bisa 100.
Rahoton ya ce kayayyakin da farashinsu ya ƙaru sun haɗa da kayan abinci da kuma abubuwan sha wanda ya kai kashi 11.42 bisa ɗari da ruwa da wutar lantarki da gas da kuma man fetur.
Sauran kayayyakin da suka tashi su ne tufafi da takalma da sauransu.
Hukumar ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo a watan Maris ɗin 2023 wanda ya kai kashi 24.45 bisa ɗari idan aka kwatanta shi da kashi 17.20 da aka samu a watan Maris ɗin 2022.
A yawan lokuta dai, ana danganta hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya saboda yawancin abubuwan da ake amfani da su a ƙasar shigowa da su ake yi.