Akalla Manyan Lauyoyin Najeriya, SAN, guda tara ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta naɗa domin kare sakamakon zaɓen shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, Abubakar Mahmoud (SAN) ne zai jagoranco tawagar lauyoyin.
Sauran mambobin tawagar sun hada da Stephen Adehi (SAN), Oluwakemi Pinheiro (SAN), Miannaya Essien (SAN), da Abdullahi Aliyu (SAN).
An tattaro daga mamba na towgar lauyoyin cewa SAN hudu wadanda ma’aikatan sashen shari’a ne na INEC suma mambobin kungiyar ne tare da Garba Hassan, Musa Attah, da Patricia Obi.
INEC ta ware sama da Naira biliyan 3 domin kare sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da na gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Ƴan takara da dama ne waɗanda su ka gadi zabubbukan da aka kammala su ka shigar da kara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe domin kalubalantar sakamon zabubbukan.