Hukumar tsaron farar hula ta ƙasa, NSCDC, reshen jihar Kwara, ta cafke wani mutum mai shekaru 42, Abdulsalam Ajibola, bisa zarginsa da yin fakewa da cewa shi soja ne, ya ke damfarar mutane wasu makudan kudade.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PRO, Olasunkanmi Ayeni, ya rabawa manema labarai a Ilorin a yau Litinin.
Ayeni ya bayyana cewa sashin bin diddigin rundunar da ke aiki da bayanai sun gano wanda ake zargin zuwa Oke-Onigbin, karamar hukumar Isin a jihar Kwara, inda aka kama shi a ranar 24 ga watan Maris.
“An zargi Ajibola da yin wani sojan gona da ya damfari wani Abdullahi Saheed kudi Naira dubu 700,000 da Ropo Gabriel kudi Naira dubu 96,000.
"Ya yi alkawarin taimaka musu su samu shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA), Kaduna," in ji Mista Ayeni.
Ya kuma ƙara da cewa har wani malamin addinin Kirista ya damfara, inda ya gudu da motar sa kirar Picnic.
Jami’in NSCDC din, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, bayan rundunar ta kammala bincike.