Ma'aikatar Harkokin Hajji da Ummara ta ƙasar Saudiyya ta shawarci alhazai da ke shirin zuwa ibadar Ummara da kada su taho da maƙudan kuɗaɗe da kuma kayayyaki masu tsada zuwa ƙasar.
A wani sako da ta wallafa shafinta na Twitter, ma'aikatar ta shawarci alhazan Ummara da kada su taho da gwala-gwalai da sauran kayayyaki masu daraja, inda ta shawarce su da kada ta su ɗauko tsayar kuɗi da ya kai Dalar Amurka dubu 16,000, wanda ya yi daidai da Riyal dubu 60,000 na Saudiya.
Hakazalika ma'aikatar ta shawarci baƙin da su sauke manhajar banki ta sahihan shafukan intanet, inda ta gargade su da kada su baiwa wani lambar asusun su na banki, ko tura wa wanda basu da alaƙa da shi kuɗi ta asusun banki, sannan su kai da kai ga duk wani sakon waya da za a rika aika musu daga lambobin da basu sani ba.
Sannan ma'aikatar ta shawarci alhazan da su gaggauta sanar da ita idan alhajin Ummara na zargin ana yunkurin damfarar sa koma an damfare shi.