‘Yan sandan na birnin California sun dauki wannan Zomo aiki ne a rundunar, bayan da suka ce sun gamsu da hazakarsa.
Hakana cikin wata sanarwa ce da rundunar ta fitar a shafinta na Facebook a shekarar 2016.
A cewar rundunar, ta yi matuƙar farin ciki game da gabatar da jami’in sanya walwala da karfafa gwiwa, ga jama’a mai suna Percy,
sanarwar da sashen hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Birnin Yuba a ranar 5 ga Afrilu zai ta ce Percy zai riƙa nishadantar da jama’a a rundunar.
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, “YCPD suna da tsarin sanya walwala ga dukkan ma’aikata da iyalansu dake aiki da rundunar shiyasa aka ɗauki Zomo Percy a matsayin babban jami’i da zai riƙa gudanar da wannan aiki.
A ɓangare guda ana saran wannan shiri zai taimaka wajen ƙarfafa guiwa ga sauran ma’aikata sannan zai ba da fiffiko kan lafiyar jiki da kwakwalwa da samar da kayayyaki da albarkatun rage gajiya tare da samar da ginshiki mai inganci ga jin dadin rayuwa.
Rahotannin sun ce sabon aikin da aka ba ofisa zomo (Percy) shi ne zai riƙa Kwanciya ko zama ko tsayuwa ko kishingiɗa a sashen ’yan sandan na birnin, saboda shi dabba ne da yaƙe da kwarewa wajen taimakawa jama’a.
‘Yan sandan birnin dai sun sanya hotunan Percy sanye da rigar aiki mai suna “Police K9” kamar yadda aka saba gani ga ’yan sanda karnuka.
Daga yanzu dai ɗan-sanda zomo Percy, mai launin ruwan kasa, tun farko dai wata ’yar sandan ce a birnin na Yuba mai suna “Ashley Carson” ta tsince shi a ranar 21 ga Oktoba shekarar 2022, kamar yadda rundunar ‘yan sandan ta bayyana.