A ranar Juma’a ne kungiyar agaji ta Qatar Charity tare da hadin gwiwar hukumar zakka da bayar da tallafi ta jihar Sokoto, SOZECOM, ta kaddamar da sabon aikinta mai taken “Shirin Tallafin Shanu ga Mabukata” a jihar.
An fara bikin kaddamarwar ne da iyalai takwas daga cikin ‘yan gudun hijirar daga Gandi da ke karamar hukumar Rabah a jihar.
A nasa jawabin, Muhammad Maidoki, Shugaban SOZECOM, ya yabawa wadanda suka samar da wannan shiri.
Maidoki ya ce tsarin wani sabon salo ne wanda zai yi tasiri matuka ga rayuwar mutane da dama wajen tabbatar da dorewar al'umma.
"Ba mu da isassun kalmomi da za mu gode wa da yawa daga cikin ayyukan da Qatar Charity ta yi wa mutanenmu, musamman marasa galihu a cikinmu.
“shirin da a ka Æ™addamar na yau kamar sauran na baya ne da muka amfana a jihar Sokoto, shiri ne wanda zai ba da damar inganta rayuwar iyali mai dorewa.
"Saboda haka, iyalai masu cin gajiyar ya kamata su kasance masu hakuri da azama, saboda sana'ar kiwo na bukatar sadaukar da kai don samun dorewa," in ji shi.